Muggan Kwayoyi a Mekziko da Afirka

Wasu daga cikin Shugabannin Afirka

Jami’an hukumar kula da hana yaduwar miyagun kwayoyin dake sa maye a Amurka, sun bada rahoto

Jami’an hukumar kula da hana yaduwar miyagun kwayoyin dake sa maye a Amurka, sun bada rahoton cewa, yanzu dillalan kwayoyi a Mexico sun juya akalarsu zuwa nahiyar Afirka a kokarin ci gaba da yin kane-kane a safarar miyagun kwayoyi zuwa kasa da kasa.

Jami’an hukumar hana saye da safarar kwayoyi masu sa maye ta Amurka sun bayyana cewar sakamakon wani dogon binciken da suka gudanar, ya nuna yadda yanzu ake jigilar sanadaran harhada kwayoyi daga kasashen Afirka zuwa Mexico domin hada kwayar a kuma maida ita zuwa Afirka daga inda ake shirya safararsu zuwa turai.

Babban jami’in kula da ayyukan hukumar ta DEA a nahiyar Afirka Jeff Breeden yace yana da isasshiyar shaidar dake tabbatar da zargin da ake yi, kuma muddin ba’a dauki wani mataki daga shiyyar shugabannin Afirka ba, abin zai sake kazancewa ne.