Muguwar Guguwar Idai Ta Janyo Barazanar Cututttuka Ga Dabbobi

Ambaliyar ruwa, sakamakon muguwar guguwar Idai a farkon watan Maris, wacce ta hallaka mutane akalla 750 a lokacin da ta afkawa kasashen Mozambique, Zimbabwe da Malawi, ta tilastawa dubban mutanen kasar Malawi zuwa sansanonin tsugunnar da jama’a. Amma kan dole suka bar dabbobin su, ciki har da shanu, da awaki, da aladu, da kaji. Hukumomi sun ce akalla dabbobi 15,000 suka mutu sanadiyar ambaliyar.

A yankin tsaunin Shire da bala’in ya fi shafa, dabbobi fiye da 4,000 ruwa ya tafi da su.

Edwin Nkhulungo, shine shugaban kula da lafiyar dabbobi na yankin. Ya ce ambaliyar ruwan ya kuma janyo barazanar cututtuka ga sauran dabbobin da suka tsira.

Ya kuma bayyana cewa, a lokacin ambaliyar, ta kai ga an sami dabbobin da suka zauna cikin laka daga dare zuwa wayewar gari kuma wannan zai kawo cututtuka, da raunuka. Haka kuma a wannan lokacin, an sami karuwar kwari da suka yi ta cizon dabbobin suna kuma daukar cuta daga wannan dabbar zuwa waccan dabbar.”

Kungiyar aikin agajin kare dabbobi ta duniya na aiki a yankunan Malawi da bala’in ya fi shafa don dakile bazuwar cututtuka a tsakanin dabbobin.