Muhimmancin Samun Auduga Mai Inganci Ga Yara Mata A Lokacin Da Suke Al'ada

Your browser doesn’t support HTML5

Bincike ya nuna daya cikin yara mata 10 a yankin kudu da hamadas Sahara ta na fashin karatu a lokacin da suke yin al'ada. Dr. Asma’u Mu'azu Muhammad, likitar mata a Abuja a babban birnin tarayyar Najeriya, tayi karin bayani akan mahimmancin dake a kwai ga yara mata su samu audugar mata mai inganci.