Yaran da har yanzu suke a kasar ukraine su na fama da lalurar damuwa sakamakon tashin hankali na yaki da suka gani.
Dr. Mohammed Mahmud Yusuf, kwararren likitan kwakwalwa a wani asibitin masu tabin hankali a Maiduguri, ya yiwa wakiliyarmu Hussaina Mohammed karin bayani a game da lalurar ta PTSD.
Kungiyoyin kasa da kasa daban-daban sun bayyana cewa yakin da ake yi a arewacin yankin Tigray na kasar Habasha zai yi mummunar illa ga lafiyar kwakwalwar mata da kananan yara. Musamman yaran da suka fuskanci yaƙi da gudun hijira a cikin kasarsu kuma suna buƙatar taimako.
Bincike ya nuna daya cikin yara mata 10 a yankin kudu da hamadas Sahara ta na fashin karatu a lokacin da suke yin al'ada. Dr. Asma’u Mu'azu Muhammad, likitar mata a Abuja a babban birnin tarayyar Najeriya, tayi karin bayani akan mahimmancin dake a kwai ga yara mata su samu audugar mata mai inganci.
A Mozambique, yara mata da yawa sun dakatar da karatun su a sakamakon daukan ciki a kananan shekaru, auren dole, fatara, cin Zarafi da lalata. Asusun bada tallafin al'ummar Amurka ya ce zai bada tallafin dala miliyan 10 har na tsawon shekaru biyar da zummar inganta illimin'yaya mata dubu dari biyu.
A Chimoio na lardin Manica dake kasar Mozambik, motsa jiki na calisthenic na taimakawa matasa su nisanci amfani da miyagun kwayoyi, da kuma zama cikin lafiya.
Dakta Abdullahi Isa, kwararren masanin cututtuka a jihar Kano, ya yi karin bayani a game da bullar cutar ta murar mashako.
Dakta Hajar Mamman Nassir, Kwararriyar Likita a Abuja, Najeriya ta yi mana ƙarin bayani a game da yadda ake magance cututtukan da akai shakulatun bankagaro da su a cikin al’ummomi daban-daban.
Masana na ganin zogale da Malambe a matsayin kayan abinci masu gina jiki dake amfani musamman ga lafiya. Abubuwa masu gina jiki dake cikin nau’ukan abincin sun zarce na sauran nau’ukan abinci, lamarin dake bada gudummawa ga lafiya a cewar masana abinci.
Kwararriya kuma ‘yar kasuwa, Maryam Idris ta amsa tambayoyi wasu mahimman tambayoyi a game da fa'idodin zogale da kuma ire-iren abincin za su iya dakile kamuwa da cututtuka.
A Ghana gwamnati ta kirkiro da wata manhaja mai suna E-PHARMACY domin saukake hanyoyin siyan magungunan bature da kawarda masu sayar da magungunan marasa inganci dake illa ga kiwon lafiyan jama'a.Ana sa ran wannan manhaja za ta taimaka sosai muddin aka kara samun annoba kamar coronavirus a nan gaba.
Dr Shema Ahmad Abdulsadiq na sashin aikin zuciya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ya yi mana karin bayani akan mai ake nufi da matsalar bugun zuciya wato cardiac arrest a turance kuma ta yaya mutum zai iya shawo kan matsalar.
Domin Kari