Mukarrabin Shugaban Turkiya Za Zama Shugaban Jam'iyyar dake Mulki

Binali Yildirim, sabon shugaban jam'iyya mai mulkin kasar Turkiya kuma wanda aka kyautata zaton zai zama Firayim Ministan Kasar

Takaddamar da ta kunno kai tsakanin firayim ministan kasar Turkiya Ahmet Davutoglu da shugaban kasar Erdogan ta kare da zaben na hannun daman shugaban a matsayin shugaban jam'iyyarsu dake mulkin kasar.

Jam'iyyar dake mulkin kasar Turkiya ta zabi Binali Yildrim wani mukarrabin shugaba Reccep Tayyip Erdogan a zaman shugaban jam'iyyar kuma watakila shi za'a ba mukamin Firayim Ministan kasar.

Mr Yildrim, shi ne ministan harkokin sufurin kasar kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar Justice and Development.

Zai maye gurbin Firayim Minista Ahmet Davutoglu wanda jiya Lahadi yayi murabus a hukunce, bayan da yayi ta fuskantar sabanin ra'ayi tsakaninsa da shugaba Erdogan.

Mr. Yildrim dan shekara sittin da haihuwa yayi takarar shugabancin jam'iyyar ba tare da hamayya ba, kuma ana sa ran zai goyi bayan burin shugaba Erdogan na yiwa kundun tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

A jawabin da ya gabatar kafin a zabeshi, Mr. Yildrim ya yi alkawarin yiwa shugaban kasar Turkiya biyayya sau da kafa.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan