Mun Kashe 'Yan Boko Haram Sama Da 1,000 Cikin Wata Biyu - Buratai

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce tun bayan da ya tare a shiyayr Arewa maso gabashin Najeriya dakarunsa sun samu nasarar halaka wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne su fiye da 1,015 a wasu kauyukan jihohin Borno da Yobe.

A dai a ranar 4 ga watar Afrilun wannan shekarar ta 2020 Buratai ya yi kaura zuwa yankin arena maso gabashin kasar.

Babban Hafsan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya shirya wata liyafar cin abinci da jami’an sojan Najeriya da suka samu raunuka daban-daban a filin daga.

Ya kuma ce sun samu nasarar tarwatsa sansanonin mayakan da dama, kuma an kashe daruruwan mayakan da suka yi yunkurin tserewa.

Ko da yake wasu sojoji 11 sun rasa rayukansu yayin da wasu kuma suka jikkata, a cewar babban hafsan.

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya yi alkawarin cewa zai ci gaba da taimaka wa jami’an sojan Najeriya wajen yakar ‘yan ta’addan.

Ya kuma yaba da irin nasororin da jami’an suka samu a cikin wata biyu da suka gabata.

Wasu daga cikin sojojin da suka jikkata a filin dagar yaki da ‘yan Boko Haram sun yaba da taron liyafar.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Mun Kashe 'Yan Boko Haram Sama Da 1,000 Cikin Wata Biyu - Buratai