Muna Hanzarin Ganin Ayyukan Noma Sun Kankama - Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Kasar Najeriya na hanzarin ganin ayyukan noma sun kankama, an samu cimaka isassa tare da samar ma miliyoyin matasa ayyukan yi

Yayinda ya karbi bakuncin Jakada Nasser Bourita, jakada na musamman daga sarkin Morocco, Sarki Muhammad VI yau Alhamis, Shugaba Buhari yace gwamnatinsa na hanzartawa cikin gaggawa ta ga ayyukan noma sun tashi domin samAr da abinci ga al'umma da kuma aikin yi ga matasa.

Shugaba Buhari yace "Mu a nan Najeriya tamkar zamu sake farawa ne tun daga kasa. Akwai lokacin da muke da dimbin arziki amma sai muka yi sakaci. Amma da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, yanzu muna sake daura damara", inji shugaban.

Shugaba Buhari ya yi na'am da nufin kasar ta Morocco ta gina masana'antar sarafa taki a Najeriya. Kamfanin takin, ba Najeriya kadai zata ci gajiyarshi ba har da ma sauran kasashen yammacin Afirka.

Jakadan wanda kuma har wa yau shi ne karamin ministan harkokin kasashen waje da hadin kai yace kasarsa ta kirkiro dabarar dakile duk wani tsatsauran ra'ayi kuma kasar tana cin nasara a yaki da ta'adanci