Muna So Biden Ya Maida Hankali Kan Tattalin Arzikin Afrika - Boube Namaiwa

Shugaba Joe Biden yana jawabi bayan daukar rantsuwa

Mai nazarin harkokin mulki a kasashen Afrika farfesa Boube Na Mewa na jami’ar Diof dake Dakar, Senegal ya bayyana cewa, a ganin sa zaben Trump babban kuskure ne.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Farfesa Boube Na Mewa, mai fashin baki akan siyasar duniya na jami’ar Diop a kasar Senegal, ya ce an fuskanci kalubale ta fannoni da dama da suka hada da annobar Korona da ta gunguntar da tattalin arzikin kasashen duniya cikin shekaru hudu da suka shige karkashin mulkin shugaba Donald Trump,

Farfesa Na Mewa ya ce babban abinda su ke so su ga sabuwar gwamnatin Amurka ta maida hankali kan farfado da tattalin arziki, da inganta dangantaka da sauran kasashen duniya da kuma tabbatar da kare damokaradiya musamman a kasashen da ake mulkin kama karya da kuma danniya a lokutan zabe.

Rantsar da Shugaban Amurka Joe Biden

Dangane da kushewar da wadansu kasashen Afrika ke yi da cewa bakaken fata na Amurka da ita kanta nahiyar Afrika basu amfana da gwamnatin tsohon shugaban Amurka Barack Obama ba, Farfesa Na Mewa ya ce, tilas ne shugaban ya mayar da hankali ga Amurka da ci gaban ta saboda kada a zarge shi da nuna wariyar launin fata.

Farfesa Na Mewa ya kuma kalubalanci al'umman kasashen nahiyar Afrika su rage zuba ido ga wasu kasashen, su yi tsayin daka su zabi shugabanni na gari wadanda zasu kawo sauyi mai kyau ga nahiyar, da kuma shugabanni masu kishin kasa. Ya ce, “shugaban wata kasa baya zuwa gina wata kasa”.

Rantsar da Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka Kamala Harris

Dangane da mulkin shugaba Donald Trump, Farfesa Boube Na Mewa ya ce a ganinsa babban kuskure ne Amurka su ka yi da zaben Trump, sabili da koma bayan da yace an samu ba a Amurka kadai ba, amma a kasashen duniya baki daya sakamakon sabanin da aka rika samu a dangantaka da huldar diplomasiya tsakanin kasashe.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya isa Florida

Farfesa Na Mewa ya bayyana cewa, Trump ya gurbata yanayi na dangataka da hulda tsakanin Amurka da kashen duniya da kuma neman gurbata demokradiya a Amurka da kokarin maida tsarin demokradiyyar Amurka ya zama kamar irin yadda ake gani a nahiya Afrika.

trump-ya-yiwa-mutane-73-afuwa-kafin-bankwana-da-kujerar-mulki

trump-ya-kammala-wa-adin-mulkinsa

Saurari cikakkar hirar Alheri Grace Abdu da Farfesa Bube Na Mewa: