Muryar Amurka Ta Sallami Ma'aikatan Sashen Hausa Sha Biyar

VOA

Muryar Amurka ta salami ko kuma tana shirin sallamar ma’aikatan sashen Hausa goma sha biyar, sabili da zargin aikata ba daidai ba da ya hada da karbar kudi da ya sabawa ka’idar aiki.

Darektar Muryar Amurka Amanda Bennett ta bayyana a sakon email da ta aikawa ma’aikata yau alhamis cewa, an shaidawa hukumomin game da zargin a cikin "watanni da suka shige", nan da nan kuma aka kaddamar da bincike.

Tace, “yayinda doka ta hanamu bada bayani dalla dalla, bayan kamala binciken ne aka dauki matakin sallama ko kuma shirin sallamar ma’aikatan.

Amanda Bennett tace “wani gwamna ne daga daya daga cikin wadannan yankunan da Sashen Hausa ke watsa shirye-shiryensa, ya bada kudin.”

Tace an kuma kaddamar da bincike domin tantance ko an watsa wadansu shirye shirye sabili da kudi da aka karba ne, kuma idan aka tarar da haka, za a dauki mataki nan take yadda ya kamata.

Bennet tace shugabannin sassan harsunan Afrika na Muryar Amurka sun bada cikakken goyon baya yayin gudanar da binciken da kuma shawarar da aka tsayar na sallama ko kuma niyyar sallamar wadanda abin ya shafa.

Malama Bennett ta kara da cewa babu abinda yake da muhimmanci a Muryar Amurka kamar amincewa da yarda da masu sauraronmu suke da ita a kanmu. Idan muna so mu kare wannan mutuncin da yardar, babu abinda yake da muhimmanci fiye da gudanar da aikinmu na ‘yan jarida bisa tsari da kuma kwarewa, da kare mutunci kamar yadda doka ta ayyana.