Musulmai A Ghana Na Ci Gaba Da Hada Hannu Wajen Tallafawa Marasa Karfi Da Kayan Buda Baki

Duk da kalubale na tattalin arziki da kasar Ghana ke fuskanta, musulmai a kasar na ci gaba da hada tallafin kayan abinci a cikin watan nan na Ramadan.

ACCRA, GHANA - Yayin da Musulmai a fadin duniya ke ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadan, lokaci ne da malamai suke karfafa gwiwar masu karfi, domin taimakawa marasa karfi.

Mallam Achiba Suleman jallo ya ce duk da kalubalen tattalin arzikin

Sarkin Ciessawan Ghana wanda a kowacce shekara ya ke shirya wa jama'a abin buda baki ya ce akalla yana kashe dala 150 a rana don shirya wa musulmai masu azumi a cikin watan Ramadana kayan buda baki.

Ramadan wata ne da ake ci gaba da karfafa gwiwar al’umma musamman masu karfi su ci gaba da tallafawa marasa karfi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hawa AbdulKarim:

Your browser doesn’t support HTML5

Musulmai A Ghana Na Ci Gaba Da Hada Hannu Wajen Tallafawa Marasa Karfi Da Kayan Buda Baki