Dan majalisar dokokin Amurka Musulmi ya kira ISIS kungiyar taron makaryata

Mayakin ISIS yana farfaganda da tsorata mutane

Wani Musulmi dan majalisar dokokin Amurka ya kira kungiyar ISIL a matsayin “taron makaryata, masu kisan kai, masu gallazawa al’umma da kuma masu fyade” bayanda kungiyar tayi barazanar kashe shi.

Dan majalisar wakilai Keith Ellison dan jam’iyar Democrat daga jihar Minnesota ya kushewa kungiyar ‘yan ta'adan cewa, babu Musulmin kwarai dake daukar koyarwarsu a matsayin addinin Islama.

Yace kasancewa bana goyon bayan kungiyar ISIS manuniya ce cewa, ina kare abubuwa kamar adalci, da hakuri, da kuma damawa da kowa a duniya, inji Ellison.

Yace kungiyar mayakan ISIS ta bata takaitaccen sunan dake nufin hadin kai.

Cikin makon nan mayakan ISIS suka fitar da wata fatawa tana yiwa wadansu mutane barazana da ta kira masu sabo a Amurka da Australia da Britain da kuma Canada.

Sun hada da Huma Abedin mataimakiyar ‘yar takarar shugaban kasar Amurka kuma tsohuwar sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen kasar Hillary Clinton.