Musulman Kudancin Kamaru Suna Goyon Bayan Shugaba Paul Biya Yayi Takara Wa'adi Na 7.

Shugaba Paul Biya na kamaru.

Gangamin da musulman suka shirya karkashin kungiyar Dattijai musulmi na kudancin kasar sunce akwai buktar Paul Biya ya ci gaba da mulmi.

Kungiyar dattijan musulmi na kudancin kamaru, harda matasa, sunyi taro inda suka amince zasu goyawa shugaban kasar Paul Biya, ya sake takara karo na 7, bayan da ya shafe shekaru fiyeda 30 yana mulkin kasar.

Shugaban kungiyar dattijan Alhaji Rilwan Sharubutu, yace sun dauki wannan matakin ne sabda baiwa shugaban damar karasa ayyukan da ya fara bai kammala ba, ga yaki da Boko Haram, da sauran ayyukan cikin kasa.

Shima shugaban kungiyar matasa musulmi a arewacin kamaru, yace wannan taro ba na musulmi na wata shiyya daya bane, illahirin musulmin jamhuriyar kamaru suna goyon bayan wannan mataki.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Musulmi suna goyon bayan Paul Biya