Mutane Da Dama Sun Mutu a Harbin-Kan-Mai-Uwa-Da-Wabi a Amurka

Jami'an tsaro suna sintiri a wurin da aka kai hari a El Paso, jihar Texas, 3 ga watan Agusta, 2019.

Kakakin ‘yan sandan yankin, Sergeant Enrique Carrillo, ya ce an kama wani mutum da ake zargi da kai harin.

Mutanen da ba a bayyana adadinsu ba, sun rasa rayukansu a wani hari-kan-mai-uwa da-wabi da aka kai a garin El Paso da ke kan iyaka a jihar Texas.

‘Yan sandan yankin sun tabbatar da aukuwar wannan hari inda suka ce an cafke mutum guda da ake zargi da kai wannan hari.

Da misalin karfe 11 na safe ne ‘yan sanda suka ce sun samu kira da rahotanni a kantin sayar da kaya na Walmart da kuma wani rukunin shagunan kasuwanci da ake kira Cielo Vista da ke gabashin birnin.

Kakakin ‘yan sanda Sergeant Enrique Carrillo, ya ce an kama wani mutum da ake zargi da kai harin.

Kafofin yada labarai sun ce mutumin wani namiji ne mai shekaru 21.

Jaridar El Paso Times da ake wallafawa a yankin, ta ruwaito Magajin Garin na El Paso yana cewa, an kama mutane uku da ake zargi da hannu a hare-haren.

Amma rundunar ‘yan sanda yankin ta ce mutum daya aka kama wanda ya bude wuta akan mutane.