Mutane Da Yawa Ba Su Fita Zaben Afghanistan Ba

An rufe rumfunan zaben shugaban kasa a Afghanistan a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazanar hare-hare daga ‘yan bindiga da kuma wasu dalilai da suka shafi tsarin gudanar da zaben.

Jami’ai sun ce mutane da yawa ba su fito kada kuri’a ba, yayin da mayakan kungiyar Taliban su ka kai wasu ‘yan hare-hare, su ka kuma yi barazanar kai hare-hare a rumfunan zabe, abinda ya sa wasu ‘yan kasar su ka ce ba za su fita kada kuri’a ba.

Ko da yake, wani dan Afghanistan, ya fadawa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa zai je ya kada kuri’arsa. Mohiuddin, ya ce ba ya jin tsoro. Ya kara da cewa ya zama wajibi su yi zabe idan su na son canji a rayuwarsu.

An baza dubban jami’an tsaro a fadin Afghanistan don kare masu kada kuri’a da kuma rumfunan zabe fiye da 4,000 a fadin kasar.

Wani jami’in ma’aikatar kula da harkokin cikin gidan Afghanistan, ya fadi cewa akalla mutane 23 su ka jikkata a ‘yan hare-haren da aka kai kan masu sakkon zuwa kada kuri’a. Ya kuma ce an dakile wasu hare-haren.