Mutane Hudu Ke Neman Kujerar Sarautar Zing dake Jihar Taraba

Sanata A'ishah Jummai Alhassan, 'yar takarar gwamnan Taraba kuma wadda yanzu tana cikin jerin sunayen ministocin Shugaba Buhari

Turmutsitsin da aka yi a Mina kasar Saudiya ranar 24 ga watan jiya yayinda alhazai ke jifar Shaidan sarkin Zing Alhaji Abbas Sambo ya rasa ransa tare da matansa biyu lamarin da ya sa yanzu wasu na neman maye gurbinsa.

Mutane hudu ne suka bayyana aniyarsu na shiga takarar neman kujerar sarautar Zing da aka sani da suna Kpanti Zing.

Sakataren gwamnatin jihar ta Taraba Anthony Jenison yace gwamnati zata bi duk sharudan da doka ta zayyana wajen zabar sabon sarkin. Yace a cikin 'ya'yan sarakunan masarautar mutane hudu ne suka rubuta wasikar neman tsayawa.

Bisa ga tsarin doka babu wani mahaluki komi girmansa da ya isa ya nada wani a matsayin Kpanti Zing. Yace dole ne a bi dokokin da aka shimfida. Yace akwai kauyuka 22 su ne suke da izinin su zabi sabon Kpanti Zing.

Gwamnatin jihar ba zata yadda da wani da aka kawo mata ba idan ba wadannan kauyukan 22 suka zabeshi ba.

Rasuwar sarkin ta haddasa zanga zangar matasan masarautar da ta tilastawa gwamnatin jihar Taraba sanarda sunan Wazirin Zing Sir Linus Ibrahim a matsayin sarki mai rikon kwarya na masarautar.

Gwamnati ta bada tabbacin cewa za'a gudanar da zaben sabon sarkin da zara kura ta lafa.

Yanzu dai gwamnatin jihar ta daki tsauraran matakan tsaro saboda tabbatar da doka da oda a masarautar yayinda kuma a ke cigba da dokar ta baci da gwamnati ta kafa tun daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane Hudu Ne Suke Neman Kujerar Sarautar Zing dake Jihar Taraba 2' 51"


.