Mutane Hudu Sun Mutu A Runfar Zabe A JIhar Kebbi

Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega a Abuja, Maris 30, 2015.

Mutane hudu sun gamu da ajalinsu a wata arangama tsakananin jami’an sojoji da masu kada kuri’a a wata mazaba dake kauyen Bayan Dutse a jihar Kebbi

Hukumomi a jihar Kebbi sun tabbatar da mutuwar mutane hudu bayan wata arangama tsakananin jami’an sojoji da masu kada kuri’a a wata mazaba dake kauyen Bayan Dutse a Karamar Hukumar Suru, a yayinda ake gudanar da zabukan gwamnoni da ‘yan majalisa.

A cewar wadansu shaidun gani da ido, mutanen garin Bayan Dutse dake karamar hukumar Suru, musamman matasa dake runfar zaben, sun zargi wani mutum da yunkurin arangizan kuri’u suka kuma dauki doka a hannunsu, suka yi mashi duka.

Bayanda ya sha da kyar daga baya ya dawo tare da motar soji da nufin kama wadanda suka doke shi, yayinda su kuma matasan suka yiwa sojojin ruwa duwatsu abinda ya sa sojojin suka bude wuta, suka bindige mutane hudu suka kashe su.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi Danladi Mishelboka ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kuma ce ana kan gudanar da bincike.

Wakilin Sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna ya aiko da rahoto cewa, banda rashin fitar jama’a, an gudanar da zaben lafiya a sauran sassan jihar.

Ga cikakken rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben zaben gwamna a jihar Kebbi-2:44