Jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma sun tuhumi dubban masu zanga-zangar da suka bijirewa dokar 'yan sanda ta hana taron zagayowar ranar fara zanga zangar nuna kin jinin gwamnati a daren ranar Talata 9 ga watan Yuni.
Mutane sun tattaru a filin Chater Garden a gundumar Tsakiya inda ake hada-hadar kasuwanci a Hong Kong da yammacin ranar Talata. Wasunsu sun rike tutocin da aka rubuta “Yancin Hong Kong" sun kuma yi ta yin wake-wake.
'Yan sandan kwantar da tarzoma da yawa sun dirar masu, suna bincikensu.
Sun fada wa taron jama'ar su bar wurin, sun kuma fada masu taron da suke yi ba bisa ka’ida ya ke ba kuma zasu kama su idan basu bi umurni ba. Wani mutum da ya zagi ‘yan sandan, nan da nan aka kama shi aka kuma tsare shi yayin da jama’ar da suka taru wurin suka yi ta rera wakokin kin jinin ‘yan sanda.