Mutum 60 Suka Mutu a Harin Rann - Kungiyar Amnesty

Wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Rann a jihar Borno kusa da iyakar Najeriya da Kamaru. Yuli 29, 2017.

Akalla mutum 60 aka kashe a wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai a garin Rann da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, inji kungiyar kar hakkin bil Adama ta Amnesty International.

A cewar kungiyar, ta samu bayananta ne daga hotunan tauraron dan Adam da ta yi kididdiga akansu, wadanda suka nuna an kona daruruwan gine-gine a garin, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Amnesty International ta ce, harin wanda aka kai a ranar 28 ga watan Janairu, shi ne mafi muni da aka kai a ‘yan kwanakin nan.

“Ta hanyar amfani da hotunan tauraron dan adam, mun tabbatar da cewa an yi kone-kone a lokacin da Boko Haram ta kai hari akan Ranna, wanda aksarinsa an daidaita shi.”

Kungiyar ta kara da cewa, da yawa daga cikin gine-ginen da aka kona, matsugunin da aka tanadarwa ‘yan gudun hijira ne, wadanda suka je neman mafaka.

Amnesty ta kara da cewa ta damu matuka bayanan da wasu shaidu suka fada mata cewa, dakarun Najeriya sun janye da kwana daya kenan a yankin aka kai harin.

Ya zuwa yanzu, hukumomin tsaro a Najeriyar ba su ce uffan kan wannan hari ba.

A na shi bangaren, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nuna takaicinsa kan harin na Rann.

“Hankulanmu da addu’o’inmu na tare da iyalai da abokanai da duka wadanda suka rasa wani nasu a wannan sabon hari akan Rann.” Atiku ya fada a shafinsa na Twitter.