N30,000 Ne Mafi Karancin Albashin Ma’aikatan Najeriya

Shugaban Muhammadu Buhari ya sa hannu kan sabuwar dokar mafi karancin albashi a Najeriya.

Shi dai wannan kuduri da yanzu ya zama doka, zai nuna a sabon tsarin biyan ma’aikatan Najeriya albashinsu.

Tun farko dai Majalisa ta amince da dokar biyan mafi karancin albashi na N30,000.

Wasu gwamnonin jihohi dai sun nuna rashin amincewarsu da wannan doka, suna mai cewa ba zasu iya biyan ma’aikatansu mafi karancin albashi na N30,000 ba.

Fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwar dake cewa shugaba Buhari ya sanya hannu a sabuwar dokar mafi karancin albashi. Daga yanzu N30,000 ne mafi karancin albashi.

Bayan dogon lokaci da kungiyoyin kwadago suka dauka suna neman Majalisun Najeriya su amince da kudirin dokar mafi karanci albashi ta N30,000 yanzu haka fadar shugaban kasa dsa ‘yan Majalisun sun amince.

Majalisar Dattawan Najeriya ta bi sahun takwararta ta Wakilai wajen amincewa da kudirin dokar Naira dubu talatin a matsayin albashi mafi karanci da za a biya ma’aikaci, bayan an kwashe lokaci mai tsawo ana gwagwarmaya da kungiyoyin kwadago.