Nahiyar Turai Ta Dara China a Yawan Masu COVID-19

Lokacin da ake duba fasinjoji domin tantance masu dauke da cutar coronavirus a China

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce yankin nahiyar turai ya wuce China a matsayin yankin da cutar coronavirus ta fi addaba a duniya.

A jiya Juma’a shugaban hukumar Tedros Ghebereyesus ya fadawa manema labarai a birnin Geneva cewa, ana ci gaba da samun karin wadanda ke kamuwa da cutar a kullum sama da abin da aka gani a China a lokacin da cutar ta tashen bazuwa.

Kasar Italiya ta bayyana a jiya Juma’ar cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu da mutum dubu 2,500 cikin sa’o’i 24 da suka gabata, abin da ya kai jimillar masu dauke da cutar a kasar zuwa 17,660.

Duk da cewa, Burtaniya ba ta cikin kasashen da Shugaba Trump ya haramtawa shiga Amurka, akwai daruruwan mutane da suka kamu da cutar a kasar da ma Ireland.

Hakan ya sa Firai Minista Boris Johnson ya fito baro-baro ya fadawa al'umar kasar gaskiya.

“Ya zama dole na fadawa al’umar Burtaniya gaskiya, iyalai da dama za su rasa masoyansu tun kafin wa’adinsu ya yi.” In ji Johnson.