Najeriya: Akwai Bukatar Tunawa Da Mata a Sabuwar Gwamnatin Buhari

Kungiyar Matan Najeriya

Mata a Najeriya sun fito don kalubalantar Gwamanatin Shugaba Mohammadu Buhari, inda su kace suna kira da ya tuna da su a lokacin da zai nada mukamai a sabuwar Gwamnatin sa, kaman yadda ya yi alkawali.

Jagorar Kungiyar Binta Kasimu ta ce hakki ne akan Baba Buhari ya yi wa mata adalci, domin yadda maza suka fito suka yi layi a lokacin za6e haka mata suka fito su ma.

Ita ma Honarabul Halima Hassan Tukur ta ce abin da Mulki ya gada shi ne a fito a nema kuma sun fito kwansu da kwarkwatar su, su fadi wa duniya domin a ba mata goyon baya su nemi mukamai kamar kowa.

Mai ba mata Shawara Barista Ebere Izendu ta ce nan gaba kadan Mata daga jihohi 36 na kasar za su fito zuwa fadar shugaban Kasa, don kai ziyara ga Uwargida Aisha Buhari da matar Mataimakinsa Dolapo Osinbajo, saboda su nemi goyon bayansu domin a basu mukaman Gwamnati kamar yadda za a ba maza.

Ta ce lokaci yayi da za a dama da su saboda kasa ta yi kyau ta zama abin alfahari ga al'ummar kasar.

Medina Dauda daga Abuja ta aiko muna da wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Akwai Bukatar Dai-Daita Sahun Mata Da Maza Wajen Mukamai 2'10"