Najeriya da China sun rabtaba hannu akan yarjeniyoyin da suka cimma

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari da na China Xi Jinping

Biyo bayan ziyarar da shugaban kasar Najeriya Muhammad Buhari keyi a kasar Sin ko China, kasashen biyu sun cimma yarjeniyoyi da dama da tuni suka rabtaba hannuwa a kai tare da alkawrin cewa zasu fara aiki nan take.

Najeriya da kasar China sun rabtaba hannu akan wasu yarjeniyoyi masu mahimmanci yayin riyarar shugaban Najeriya Muhammad Buhari a kasar ta Sin.

Wasu daga cikin yarjejeniyoyin ya kamata a ce sun fara aiki tun lokacin gwamnatin da ta shude inda Najeriya ta cika nata alkawarin.

Firimiyar kasar ta China ya tabbatar wa Shugaba Buhari cewa nan ba da jimawa ba za'a fara aiki da yarjeniyoyin domin tabbatar da Najeriya ta samu wadatacciyar wutar lantarki. Za'a kuma samarda layin dogo da kuma gyara tasoshin jiragen ruwa da na jiragen sama.

Shi ma shugaban Najeriya Muhammad Buhari yace ba da bata lokaci ba Najeriya zata cika nata bangaren alkawarin na yarjejeniyar domin a fara aiki gadan gadan.

Wani masani Malam Sha'aibu Idris yace cika alkawarin Najeriya ta doshi hanyar fita daga kangin rashin wutar lantarki da kasar ke fama dashi. Yace kasashe sukan zauna su ga menene zai zama masu alfanu da zasu yi tare. A lokacin shugaba Jonathan kasar Sin ta amince ta ba Najeriya bashin nera miliyan dubu talatin amma sai Najeriya ta kasa cika nata alkawarin. Ganin haka ne ya sa kasar Sin ta ja baya.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya da China sun rabtaba hannu akan yarjeniyoyin da suka cimma - 3' 56"