Najeriya: ECOWAS, MDD, Sun Tunatar Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya Da Aka Kulla

Wani taron kungiyar ECOWAS da aka yi a Abuja a ranar 16 ga watan Afrilun 2018

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS ko kuma CEDEAO, da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU da kuma Majalisar Dinkin Duniya, sun yi kira ga jam’iyyun siyasa da wadanda ba su gamsu da sakamakon zaben shugaban kasar da aka sanar ba, da su bi hanyar da dokar Najeriya ta shimfida wajen bin kadinsu.

Kungiyoyin da Majalisar ta Dinkin Duniya sun bayyana hakan ne a wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar gabanin sanar da sakamakon zaben na Najeriya.

“Muna kira ga dukkan jam’iyyu da wadanda ke da korafi, da su bi hanyoyin da doka ta shimfida domin bin kadinsu, kamar yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma kamar yadda aka rattaba hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ta ranar 13 ga watan Fabrariru.” Sanarwar ta nuna.

Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyya mai mulki ta APC, ya sake samun wa’adi na biyu na tsawon shekaru hudu bayan da ya samu kuri’u miliyan 15, 191, 847 a zaben da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Shi kuwa babban abokin hamayyarsa, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u miliyan 11, 262, 978.

Tun kafin a ayyana sakamakon zaben jam’iyyar ta PDP ta ke neman da dakatar da kidayar kuri’un da ake yi, tana mai cewa an tafka magudi a wasu jihohi a lokacin zaben.

Amma kiran na PDP bai yi tasiri ba, inda shugaban hukumar zaben Najeriya INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce korafin na PDP bai yi girman da zai sa a soke zaben ba.