An Bukaci Gwamnatin Najeriya Ta Rika Tantance Kwarewar Masu Sayar Da Magunguna

Amfani da miyagun kwayoyi na kawo rarrabuwan kawuna tsakanin iyali, inda wasu lokutan ta kan kai ga kisa ko yiwa iyaye rauni.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta zamanto ruwan dare a fadin Najeriya, har ta kai ga gwamnati ta fara daukar matakan shawo kan lamarin.

Ganin yadda aka mayar da maganin tari ake amfani da shi don shiga yanayi na maye, ya sa gwamnatin Najeriya ta hana shigowa ko sarrafa duk wani ruwan maganin tari da ke dauke da sinadarin Codeine.

A wata hira da ta yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, tsohuwar ‘yar jarida Amina Maigadi, ta yi kira ga gwamnati da ta dauki kwararan matakai wajen sake tsarin bayar da lasisin sayar da magani ga masu shaguna.

Haka kuma a tabbatar da cewa duk wani da zai sayar da magani kwararre ne, a kuma saka ido ga masu sayar da magungunan da lokacin amfaninsu ya wuce.

Domin karin bayani saurari hirar Amina Maigadi da Alheri Grace Abdu.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci Gwamnatin Najeriya Ta Rika Tantance Kwarewar Masu Sayar Da Magunguna - 4'01"