Najeriya ta kaddamar shirin tara binciken kwakwa kan cutar HIV

Dakin binciken kwakwa

Gwamnatin Tarayyar Najariya ta kaddamar da shirin tantance binciken kwakwa da tara bayanai da zai taimaka wajen samar da magungunan kanjamau

A yunkurinta na inganta dakunan binciken kwawa da kuma ayyukan jinya a kasar, Gwamnatin Tarayyar Najariya karkashin ma’aikatar lafiya ta Tarayya tare da hadin guiwar cibiyar dakunan binciken kwawa na Najeriya, ta kaddamar da wani shirin tantance dakukan binciken kwakwa da kuma tara bayanai da zai taimaka wajen samar da magungunan cututuka.

Daga cikin muhimman bangarorin da za a maida hankali a kai, akwai, nazarin kwayar cutar HIV mai haddasa cutar kanjamau, da kuma tantance bayanan dakunan binciken kwakwa kan cutar da zata taimaka wajen horas da masu sa ido kan ci gaban da ake samu a yaki da cutar, da za a yi tare da tallafin Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma cibiyar yaki da cututuka ta Amurka.

Ministan lafiya na kasa Farfesa Onyebuchi Chukwu ya bayyana cewa, tantance cibiyoyin binciken zai taimaka wajen inganta ayyukan jinya. Bisa ga cewarshi, shirin kuma zai kunshi karfafawa dakunan binciken guiwa domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Farfesa Chukwu ya yabawa gwamnatin Amurka domin goyon bayanta wajen ganin ingancin ayyukan jinya a Najeriya musammam a wannan lokacin da kasashen duniya ke fuskantar komadar tattalin arziki. Bisa ga cewarshi, wannan gagarumin sadaukar da kai ne.

Ministan harkokin lafiyan ya hakikanta cewa, shirin zai taimaka wajen inganta matsayin dakunan binciken kwakwan Najeriya ba a cikin kasar kadai ba, amma har a matakin kasa da kasa.