Accessibility links

An sami karuwar yara dake dauke da cutar Polio a Najeriya


Wani yaro da ciwon inna ya gurgunta

Rahoton ayyukan lafiya a Najeriya na shekara ta dubu biyu da goma sha daya na nuni da cewa an sami karuwar yaduwar ciwon shan inna a kasar.

Rahoton ayyukan lafiya a Najeriya na shekara ta dubu biyu da daya na nuni da cewa an sami karuwar yaduwar ciwon shan inna a kasar. Darektan cibiyar kiwon lafiya matakin farko na kasa a Najeriya Dr. Ado Muhammad ne ya bayyana haka yayin gabatar da rahoton ayyukan cibiyar na shekarar da ta gabata.

Dr. Muhammad ya bayyana cewa, an sami kananan yara 47 dake dauke da kwayar cutar shan inna a karshen mako na hamsin da daya na shekara ta dubu biyu da goma sha daya akasin yara goma sha biyar da aka samu a daidai wannan lokacin a shekara ta dubu biyu da goma. Dr Muhammad yace an sami kwayar cutar a tsakanin yara dari bakawai da casa’in da uku a shekara ta dubu biyu da takwas, aka kuma samu raguwarta zuwa dari uku a shekara ta dubu biyu da tara, yayinda a shekara ta dubu biyu da goma aka sami kwayar cutar a jikin yara ishirin da daya.

Darektan ya bayyana cewa, dukan yaran dake dauke da kwayar cutar suna jihohi takwas na Najeriya, bisa ga cewarshi, ba a sami ko yaro daya da wannan cutar ba a tsakanin jihohi goma sha bakwai zuwa sha takwas cikin shekaru biyu da suka shige.

Dr. Muhammd ya bayyana dalilin wannan koma baya da suka hada da zabuka da aka gudanar a shekarar da ta gabata wanda ya dauke hankalin hukumomi, da sauyin shugabanni da rashin sa ido kan ayyukan rigakafi. Bisa ga cewarshi, duk da yake cibiyar ta bada dukan goyon baya da kayan aikin da ake bukata domin gudanar da aikin a matakin kasa, lamarin ba haka yake a matakin jihohi da kananan hukumomi ba, abinda kuma ya sa aka kara samun yawan mutanen dake dauke da kwayar cutar ke nan. Banda haka kuma an sami sababbin gwamnoni da shugabannin kananan hukumi, sabili da haka ya zama dole a sake daukar matakin wayar masu da kai kan muhimmancin kara kaimi a yaki da cutar.

Darektan cibiyar lafiya matakin farko na Najeriya yace zasu tuntubi shugaban kungiyar gwamnonin arewacin kasar domin ganin yadda zasu iya hada hannu da gwamnonin wajen yakar cutar kasancewa dukan jihohin da aka sami cutar suna arewa ne.

XS
SM
MD
LG