Najeriya Tana Baya A Jerin Kasashen Da Aka Sami Raguwar Mutuwa Ta Cutar HIV

HIV

Wani sabon rahoto ya nuna cewa Najeriya ita ce kasa ta karshe a cikin kasashen da aka sami ci gaba a fannin yaki da cutar kwayar kanjamau inda ake kokarin rage yawan mutane masu mutuwa ta wajen cutar HIV.

Wanan sabon rahoton da aka rubuta kan ci gaban da aka samu a fannin yaki da yada kwayar cutar kanjamar daga uwa zuwa jariri da nufin ceton uwar da kuma jaririn da nufin shawo kan yada cutar a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar ya bayana cewa, Najeriya tana bayan kasashen Lesotho, Demokradiyan Congo, Cote d’Ivoire, Chadi, da
Angola a fannin raguwan yawan mutane masu mutuwa ta wurin cutar HIV.

Bisa ga rahoton da Hukumar Lafiya ta Duniya (W.H.O) ta rubuta bayan binciken da ta gudanar, sauran kasashe kamar Botswana, Malawi, Ghana, da South Africa sun nuna alamar raguwan yawan masu mutuwa ta wajen cutar HIV ama Najeriya tana baya sosai.
Kwanan baya darektan cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Najeriya Prof Idoko ya yi kira da a kara yawan kudin da ake kashewa a aikin yaki da kwayar cutar kanjamau domin a sami nasara.