Najeriya: Yadda Hukumar EFCC Ke Daukar Hotan Wadanda Take Zargi

Tambarin hukumar EFCC

Ana ci gaba da yin mahawara kan yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ke mikawa wadanda take tuhuma kwali ko allo dake rubuce da laifi maimakon tuhuma da ake musu, kuma su daga a dauki hotonsu.

Yayin da ‘yan Najeriya ke ganin abin da hukumar EFCC ke yi daidai ne, wasu na cewa ba haka bane, domin kotu ce kadai za ta iya tabbatar da laifi bisa tsarin dokokin Najeriya.

Da yake magana da Muryar Amurka Ministan matasa da wasanni Solomon Dalung, ya nuna damuwa ga al’adar tausayawa mutanen da ake tuhuma.

Shi kuma lauya mai zaman kansa Aminu Gamawa, cewa yayi ya kamata gwamnati ta dinga yin adalci wajen hukunta kowa don gudun zargi. Haka kuma ya ce idan har gwamnatin Najeriya da gaske take wajen yaki da cin hanci da rashawa, to tabbas sai anyi aikin ba sani ba sabo.

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya tabbatar da cewa hatta a cikin jami’ansu basa barin baragurbi, domin yanzu haka akwai jami’an da suka kora, wasu kuma suna kotu.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Yadda Hukumar EFCC Ke Daukar Hotan Wadanda Take Zargi - 2'47"