An Kammala Taron Manoman Najeriya

FILE - A farmer plows the field in Saulawa village, on the outskirts of Nigeria's north-central state of Kaduna.

Taron na kwana hudu da Kano ta karbi bakuncinsa ya samu shugabancin ministan harkokin noman Najeriya Chief Audu Ogbe

Kungiyoyin manoma da masu samar da kayan noma da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin noma daga sassan Najeriya suka halarci taron.

Alhaji Salim Sale Muhammad shugaban kungiyar manoma alkama ta Najeriya ya bayyana makasudin zuwansu taron. Yace suna son su tabbatar lalle lalle sun samu damar shuka alkama a Najeriya ta kai koda kashi 50 bisa dari na wadda ake shigo da ita daga kasashen waje. Yace akwai siyasa a batun alkama. Manyan kasashen duniya da suka yi nisa ba sa son a daina sayen tasu alkamar. Matsala ta biyu ita ce rashin kyakyawar manufa daga gwamnati akan alkama.

Haka ma manoma masara sun yi amunna da taron. Alhaji Munkaila Garba shi ne shugaban kungiyoyin dake noma masara a jihar Kano yace taro ya yi. Sun amince da shirin bada taki kai tsaye ga manoma domin ita ce hanya mafi dacewa.

Hon. Munir Babba Dan Agundi da ya wakilci shugaban kwamitin harkokin noma na majalisar dokokin tarayya ya bayyana rawar da majalisar zata taka wajen tabbatar da abubuwan da aka tattauna a wurin taron.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: Yau aka kammala taron noma na shekara shekara a Kano- 3' 31"