Najeriya Zata Rage 'Yawan Masu Yiwa Kasa Hidima-NYSC

Shugaba Muhammadu Buhari

Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima watau NYSC tace rashin kudi ne yasa ta dauki wnanan mataki.

Hukumar kula da masu yiwa kasa hidima NYSC, tace zata takaita yawan masu yiwa kasa hidima zuwa dalibai dubu dari uku kadai, daga cikin kusan dalibai dubu dari biyar ko wace shekara.

Hukumar ta dauki wannan mataki ne saboda karancin kudi. Amma duk kokarinda wakilin Sashen Hausa Jibril Babangida yayi, na magana da shugabannin hukumar ya ci tura.

'Yan Najeriya da dama sun bayyana rashin jin dadinsu na daukar wannan mataki. Sun shawarci hukumar ta nemi hanyoyi da kaucewa daukar wannan mataki.

Wannan hukuma dai an kafa ne shekaru 40 da suka wuce zamanin gwamnatin Janar Yakubu Gowon, da zummar hada kan 'yan Najeriya.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rage masu yiwa kasa hidima