Neymar ya yi Jinyar Makonni Takwas Bayan Raunin da ya Samu a Idon Sawun

Your browser doesn’t support HTML5

PSG ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin tana mai cewa dan wasan mai shekaru 29 ya kuma yage jijiyoyin sawun sa. Shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin raunin da ya faru.
Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain, Neymar, zai yi jinyar makwanni takwas sakamakon raunin da ya samu a kafarsa ta hagu.

An dauke Neymar daga kan gado a wasan da shugaban gasar Faransa ya doke Saint-Etienne da ci 3-1 a ranar Lahadi.

PSG ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin tana mai cewa dan wasan mai shekaru 29 ya kuma yage jijiyoyin sawun sa.

Shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin raunin da ya faru.

A watan Disambar da ya gabata ne Neymar ya tashi daga wasan saboda raunin da ya samu a kafar sa ta hagu.

Tun lokacin da ya koma PSG a shekarar 2017 kan kudi Yuro miliyan 222 (dala miliyan 250), ya kuma samu raunukan hakarkari, makwancin gwaiwa da kuma karya kafarsa ta dama a watan Fabrairun 2018.