Niger: Annobar Coronavirus Ta Sauya Lamura A Azumin Bana

A yayin da al’ummar musulmi a kasashe daban daban suka fara azumin Ramadan a jamhuriyar Nijer majalisar musulunci ta bukaci musulmin kasar su hakura da taron sallar Tarawih da Nafilolin da aka saba gudanarwa a irin wannan lokaci a kowace shekara sakamakon anobar coronavirus da ake fama da ita.

Kamar sauran kasashe, al’ummar musulmin jamhuriyar Nijer ta dauki azumi a yau Juma’a 24 ga watan Afrilu dake dai dai da ranar 1 ga watan Ramadan bayan da majalisar malamai ta Conseil Islamique a daren jiya ta bada sanarwar ganin jaririn watan a wasu yankunan kasar.

Azumin bana na Ramadan ya zo a wani lokaci da kasashen duniya ke fama da annobar cutar coronavirus, lamarin da ya sa gwamnatoci kafa wasu dokoki musamman da zummar dakile yaduwar wannan bala’i abinda kuma ya sa majalisar malaman da wasu kungiyoyin musulunci yin kira ga al’ummar musulmin Nijer da su hakura da dukkan wani taron sallar Tarawih da Nafilolin da aka saba gudanarwa a irin wannan lokacin na yawaita ibada.

Dogara akan wasu kwararan hujjoji a musuluce ne ya sa malamai magada annabawa bullo da wadanan shawarwari.

A yau Juma’a wunin farko na watan na ramadan an wayi gari cikin tsauraran matakan tsaro a birnin Yamai ganin yadda a makon jiya aka fuskanci tarzoma a wasu unguwanni sanadiyar kosawa da dokar hana sallar Juma’a dake matsayin wani bangare na matakan da hukumomi suka dauka na dakile yaduwar cutar corona a wannan kasa.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Niger: Annobar Coronavirus Ta Sauya Lamura a Azumin Bana