Nigeriya Tana Kan Hanyar Shawo Kan Cutar Ciwon Shan Inna

UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara UNICEF ta bayyana cewa Nigeriya tana kan hanyar shawo kan cutar ciwon shan inna.
Asusun tallafawa kananan yara UNICEF ta bayyana cewa Nigeriya tana kan hanyar shawo kan cutar ciwon shan inna.

Wakiliyar UNICEF a Nigeria, Mrs Jean Gough ce ta bayyana haka a Sokoto wajen wani taron ‘yan jarida kan yaki da cutar shan inna kan shirin rigakafin allurar cutar shan inna na kwatar karshe.

Wakiliyar asusun UNICEF ta bayyana cewa, idon duniya yana kan Nigeriya yayin da kasar take kan hanyar shawo kan cutar ta kuma ce dole ayi kokari sosai a wannan sashin domin cinma nasara domin bisa ga cewarta cutar shan inna babbar muguwar cuta ce mai kashewa kuma.

Gough ta kara cewa asusun UNICEF yana shirye ya ci gaba da ayyukan a wadansu sassan kamarsu yaki da rashin abinci nagari, samar da ruwan sha da kuma tsabtace muhalli.