Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Aikin Rigakafi A Arewacin Najeriya Suna Fargaban Hari


Wata ma'aikaciya tana raba maganin rigakafin shan inna

An fara aikin rigakafin shan inna a jihar Kano dake arewacin Nigeriya. Jihar tana shirin yiwa kananan yara miliyan 3 domin kiyaye su daga cutar shan inna da kuma bakon dauro.

An fara aikin rigakafin shan inna a jihar Kano dake arewacin Nigeriya. Jihar tana shirin yiwa kananan yara miliyan 3 domin kiyaye su daga cutar shan inna da kuma bakon dauro. An dauki matakan tsaro sosai saboda kare lafiyar ma’aikatan.

‘Yan bindiga da ake tsamnai ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kaiwa wadansu mata da suke aikin allurar rigakafi a jihar Kano suka kashe mata ma’aikatan lafiya guda 9 lokacin da suke aikin yiwa yara allurar rigakafi ta gida – gida, a watan biyu a cikin garin Kano.

Sakataren shirin rigakafin na jihar Kano Dr. Shehu Usman Abubakar ya bayyanawa yan jarida cewa, wannan lokacin allurar rigakafin za’a yi ta a kauyuka dubu biyu da dari bakwai domin tabbatar da kare lafiyar kananan yara.

Yace yara 200 suka mutu a kano domin cutar bakon dauro shekarar da ta wuce.
UNICEF tace Nigeriya ta kusa kawar da cutar shan inna. Sai dai tace har yanzu akwai kananan yara 14 da aka samu dauke da kwayar cutar a watan da ya wuce.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG