Nijar: Jam'iyyar MNRD ta tsayar da Mahamman Usman takarar shugaban kasa

Kasar Jamhuriyar Nijar

Jam'iyyar MNRD Hankuri a kawancen jam'iyyu hamaya ita ce ta yanke shawarar tsayar da tsohon shugaban kasa Muhamman Usman a matsayin dan takararta na zaben 2016

Jam'iyyar ta dauki wannan matakin ne domin ta huce wa shi Muhamman Usman takaicin shari'ar da ta ki ci ta ki cinyewa.

An dai kwashe fiye da shekaru uku ana tafkawa tsakaninsa da bangaren Abdul Labo dangane da cancantar shgabancin CDS Rahama wadda a karkashinta ne ya dare kujerar shugabancin kasar a 1993.

Mataimakin shugaban MNRD Hankuri Allhaji Saidu Yakuba ya bayyana cewa irin siyasar da ake yi yanzu ana son a kawo tarnaki da wasu manyan 'yan siyasar kasar su zo su taka rawar gani a zabe mai zuwa musamman ma Mahamman Usman. Tsarin dokokin jam'iyyarsu ya basu damar dauko dan takara daga jam'iyyarsu ko kuma daga wani wurin.

Sabo da haka tunda shekarun shugabansu Alhaji Sidi Mulai Hambali basu kai ba inda zai yi takarar sai suka yi nazarin kiran Mahamman Usman ya tsaya.

Sarkin yakin kawancen adawa kuma kusa a jam'iyyar CDS Rahama bangaren tsohon shugaban kasa Alhaji Dudu Muhammadu ya tabbatar da cewa sun yaba kuma sun karbi tayin. Yace ita jam'iyyar CDS gaba dayanta Muhammadu Usman ya mallaketa kuma dimbin jama'a dake goyon bayansa yanzu suke farin ciki, suke murna.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Jam'iyyar MNRD ta tsayar da Mahamman Usman takarar shugaban kasa - 2' 48"