Jamhuriyar Nijar: Kungiyar Likitoci Sun Koka Akan Matsalolin Da Su Ke Addabar Su

Ministan Kiwon Lafiyar Nijar, Dr. Iliassou Idi Mainasara

Kwararrun likitoci a Jamhuriyar Nijar sun yi kira da Gwamnati da ta tashi tsaye domin magance irin matsalolin da su ke addabar su.

Kungiyar kwararun likitoci a Jamhuriyar Nijar, ta bukaci hukumomin kasar su gaggauta daukan matakai don magance wasu matsalolin da su ka addabi magoya bayanta, a lokacin da su ke gudanar da aiki, ciki kuwa har da barazana da rayuwar da jami’an kiwon lafiya ke fuskanta a wasu yankunan kasar.

Matsalar tsaron da ake fama da ita a yankunan Diffa da Tilaberi na daga cikin batutuwan da kungiyar Symphamed ta bayyana damuwa akansu, a cikin wata sanarwar da ta fitar bisa la’akari da yadda lamarin ke haddasawa likitoci cikas a lokacin da su ke gudanar da aikinsu.

Dr Habou Abdourhaman, shine sakataren tsare tsare na wannan kungiyar ya ce, an hana yawo da motoci da daddare, saboda an kafa dokar ta baci, inda likitocin basa iya fita da daddare domin zuwa gurin aiki, da kuma irin barazanar da su ke fuskanta daga gurin bata gari.

Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma :

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar: Kungiyar Likitoci Sun Koka Akan Dokar Ta Baci Da'aka Kafa A Wasu Yankunan Kasar