Nijar Ta Karkasa Hafsoshinda Take Zargi Da Juyin Mulki A GidajenFursina Daban Daban.

Mr.Morou Amadou, minisatan shari'a a Nijar.

Wannan mataki ba zai rasa nasaba da matsin lambar da gwamnatin take sau daga kungiyoyin kare hakkin Bil'Adama.

A ranar Laraba ne dai rahotanni daga jamhuriyar Nijar suka yi nuni da cewa gwamnatin kasar ta karkasa hafsoshin sojin da ake yiwa zargin kulla makarkashiyar kifar da gwamnatin Muhammadu Isouffu, zuwa gidajen kaso daban daban a cikin kasar.

Kafin ta dauki wannan mataki dai, wadannan mutane suna gidajen wakafi ne na rundunar jami'an tsaron kasar da ake kira jandarma.

Ana ganin gwamnatin ta dauki wannan matakin ne sakamakon matsin lamba da take fuskanta daga kungiyoyin kare 'yancin Bil'Adama da kuma na lauyoyin kasar, cewa, yadda take ci gaba da tsare mutanen ya sabawa 'yancin Bil'Adama da kuma dokokin kasa.

Sakamakon wannan mataki, Janar Salou Jalloh, wanda ake kallon a zaman madugun juyin mulkin, yanzu a maida shi gidan fursinan Kolo, mai tazarar kilomita 30 daga birnin Niamey.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Nijar ta karkasa 'yan juyin mulki a gidajen kason kasar.