Nijar Ta Sake Shiga Kungiyar Kasashe Masu Ma'adanai

Bukin Komawar Nijar Kungiyar Ma'adanai Ta Duniya (ITIE)

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta bayyana komawar kasar cikin kungiyar kasashe masu arzikin ma'adanai ta duniya wato ITIE. Hukumonin kasar sun jaddada cewa kasar za ta yi matukar amfana da komawa kungiyar.

A yau Litini aka yi bukin mayar da Jamhuriyar Nijar cikin kasashe mambobin kungiyar ma'adanai ta duniya ITIE, wacce a bara ta dakatar da Nijar, saboda zargin ta da rashi wallafa yadda take gudanar da harkokin ma’adanan ta.

Lamarin da a wancan lokacin ya fusatar da gwamnatin kasar ta yanke shawarar tsinke hulda da wannan kungiyar, saboda rashin gamsuwa da hujjojin da ta bayar na dakatar da kasar.

Framininstan Nijar Birgi Raffini, ya ba da sanarwar komawar kasarsa a cikin mambobin kungiyar ma'adanai ta duniya ITIE a gwamnatance, abin da ya kawo karshen tsamin dangantaka tsakanin bangarorin biyu.

Ministan albakatun Man Fetur a Nijar Foumakoye Gado ya ce, su na neman masu hannu da shuni da su zo su saka jari a harkokin ma’adanan kasar, domin binciko irin ma’adanan da su ke dashi a kasar.

Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Farfadowar Huldar Dangantaka Tsakanin Jamhuriyar Nijar Da Kungiyar Ma'adanai Ta Duniya ITIE