NOMA TUSHEN ARZIKI: Tinubu Ya Ce Zai Ci gaba Da Samarwa Manoma Tallafi Da Dabarun Inganta Noma, Kashi Na Shida - Agusta 01, 2023

Mohammed Baballe

Shirin na wannan makon, zai kawo muku kashi na shida na ci gaba da tattaunawa da shugabannin kungiyoyin manoma mata da maza a Najeriya wanda suka koka cewa tsohuwar gwamnatin Buhari ta ba da umarnin a basu tallafi domin su yi noma har su ciyar da kasa sannan a sayar wa wasu kasashen duniya, amma tallafin bai kai gare su ba.

Sai dai sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya ce zai ci gaba da samarwa manoma tallafi da dabarun inganta noma, domin kasar ta yi dogaro da kanta.

Saurari shirin cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

NOMA TUSHEN ARZIKI: Tinubu Ya Ce Zai Ci gaba Da Samarwa Manoma Tallafi Da Dabarun Inganta Noma 6'50.mp3