Ofishin Jakadancin Amurka Ya Yiwa 'Yan Jarida Bita Kan Zaman Lafiya

Taron bitar zaman lafiya da aka shiryawa 'yan jarida a Plato

Hukumar wanzar da zaman lafiya da sasanta al’umma a jahar Pilato ta shirya taron bita wa ‘yan jarida kan yadda zasu gudanar da aikinsu da zai taimaka wajen samar da zaman lafiya, maimakon ruruta wutar rikici.

Taron bitar wanda ya sami tallafin ofishin jakadancin kasar Amurka a Najeriya, ya kara tunatar da ‘yan jarida daga kafofin watsa labarai na ciki da ketare kan muhimmancin hadin kan al’umma.

Shugaban hukumar wanzar da da zaman lafiya a jahar Pilato, Joseph Lengman yace ‘yan jarida na da gagarumin gudummowa wajen samadda zaman lafiya da bukasar kasa.

Mahalarta taron da Sashen Hausa ya yi hira da su sun bayyana cewa, sun karu sosai.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji.

Your browser doesn’t support HTML5

Bitar zaman lafiya-3:00"