Onnoghen Ya Ajiye Aikinsa

ABUJA: Chief Justice Onnoghen of Nigeria

Babban Alkalin Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da aka dakatar, ya yi murabus daga mukaminsa.

Wasu majiyoyi da Muryar Amurka ta zanta da su, sun tabbatar da aukuwar hakan.

Kafofin yada labaran Najeriya ma da dama sun ruwaito murabus din Onnoghen a jiya Juma'a.

Rahotannin sun ce, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Abba Kyari ne ya karbi wasikar murabus din da Onnoghen ya aika wa fadar shugaban kasa.

Wasu alkalan kotun kolin kasar ne suka mika wasikar.

A farkon shekaran nan kotun tabbatar da da’ar ma’aikata ta Code of Conduct Tribunal, ta fara tuhumar Onnoghen da laifin kin bayyana daukacin kadarorinsa tare da mallakar wasu asusu a kasashen waje.

Wannan tuhuma ta sa aka dakatar da Onnoghen daga mukaminsa.