Paul Kagame Zai Sake Tsayawa Takara a Karo Na Uku

Paul Kagame

Babban kotun kasar Rwanda ta baiwa shugaba Paul Kagame damar sake tsayawa takaran shugabancin kasar

Babban kotun kasar Rwanda ta baiwa shugaba Paul Kagame damar sake tsayawa takaran shugabancin kasar zagaye na ukku har na wani tsawon shekaru 7, idan waadin mulkin sa ya kare a shekarar 2017.

Hujjar da kotun ta bayar ko shine tunda dai dokar kasar ya amince da gyara, wanda ya cire tsarin takara sau biyu kurun ga shugaban kasar ya halarta, tunda ko yin hakan bai saba wa dokar kasar ba.

Jamiyyar adawa ce ta Green Party tun farko ta shigar da kara domin hana yunkurin da majilisar dokokin kasar tayi na samar da dokar data baiwa shugaba Kagame damar sake tsayawa takara.

To sai dai hakan ba zata yi nasara ba sai idan jamaar kasar masu jefa kuria sun jefa kuriaar amincewa da wannan sabuwar dokar.

Sai dai ba mamaki wannan dokar na iya samun nasarar da ake bukata ganin irin farin jinin da shi shugaba Kagame yake dashi kana da irin tasirin sa ga kafafen yada labarai na kasar, musammam ma ganin irin yadda ya tabbatar an samu zaman lafiya tun karshen kisan kiyashin da aka yi a kasar a shekarar 1994.