PDP Ta Sha Gaban APC A Adamawa

Babban Taron Jam'iyyar PDP Na Kasa

Kamar sauran jihohi yanzu haka,an samu sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun kasa a jihar Adamawa, jihar da dan takarar babbar jam’iyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya fito.

Jam’iyar ta PDP ita ta samu galaba akan jam’iyar APC da ke mulki a jihar da kuma Najeriya.

A sakamakon zaben jihar Adamawan, jami’in ba da sakamakon zaben, Farfesa Andrew Haruna, ya bayyana jam’iyar PDP da cewa ita ke kan gaba da kuri’u mafi rinjaye inda dan takarar babbar jam’iyar PDP Atiku Abubakar ya samu kuri’u 410,266.

Sai dai wakilin jam’iyar APC, a wajen karbar sakamakon, wanda ma shi ne shugaban jam’iyyar a shiyyar arewa maso gabas, Kwamared Mustapha Salihu, ya ki ya rattaba hannu akan sakamakon zaben.

Sakamakon na Adamawa dai ya zo wa wasu da mamaki, kasancewar jam’iyyar APC ke mulki a jihar kuma ta rasa wasu kujerun majalisar wakilanta da kuma na dattawa, wanda kuma lokaci ne kawai ke iya tabbatar da yadda za ta kaya a zaben gwamna da ke tafe.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz:

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Ta Sha Gaban APC A Adamawa - 3'46"