PDP Ta Tsawaita Wa’adin Sayen Takardar Neman Takarar Shugabancinta

Sanata Ahmadu Makarfi shugaban PDP na riko da wasu mukarrabansa

Kamar yadda jam’iyyar ta sanar daga ranar 19 zuwa 30 na wannan watan Nuwamba masu neman mukaman shugabancin jam’iyyar na kasa na da zarafin sayen takardar tsayawa takara

Duk mai son tsayawa takarar neman mukamin shugabanci a jam’iyyar adawar Najeriya, PDP, yana iya yin hakan tsakanin 19 zuwa 30 na wannan watan.

Dayo Adeyeye jami’in watsa labarun jam’iyyar ya sanar da hakan. Za’a yi zabukan ne lokacin babban taron jam’iyyar da za’a yi ranar tara ga watan gobe, Disambar wannan shekarar.

Alhaji Aliyu Musa Manji daga jihar Taraba wanda ya sayi takardar neman zama mataimakin shugaban jam’iyyar na arewacin Najeriya yace lokacin aikin dora ko nadi ya wuce. Mukamin da yak enema,na mataimakin shugaban jam’iyyar na arewacin Kasar y ace an kashe arewa maso gabas ne. Akwai jihohi shida a yankin duk wanda aka zaba shi zai rike mukamin. Alhaji Manji nada karfin gwiwar cin zaben sai dai idan Allah bai bashi ba, a cewarsa. Ya kara da cewa jam’iyyarsa zata koma kan karagar mulki a zabe mai zuwa.

Shi ma Inuwa Garba mai taimakawa shugaban Majalisar Dattawan Najeriya nada irin kwarin gwuiwar Alhaji Manji. Y ace Allah ya jarabesu da cin zabe da kuma faduwa zabe saboda haka zasu tashi.

Amma a cewar APC jam’iyyar dake mulkin kasar ta bakin sakatarenta na kasa Mai Mala Boni yace zamanin neman zabe da kudi ya kare. Ya tun cin zaben Shugaba Muhammad Buhari a shekarar 2015 maganar tasirin kudi a cin zabe yak are. Injishi, siyasar kudi ta mutu a Najeriya.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

PDP Ta Tsawaita Wa’adin Sayen Takardar Neman Takarar Shugabancinta - 2' 50"