Pompeo Ya Zargi China Da Satar Fasahohin Yankin Kudancin Amurka

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo

Irin harkokin kasuwancin da China ke yi a yankin Kudancin Amurka, na da babbar alaka da manufofin tsaron kasarta da burinsu na bunkasa fannin kere-kerensu zamani da kuma satar fasahohi.”

Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya ce al’umar kasar Venezuela ta dawo daga rakiyar shugaba Nicolas Maduro da gwamnatinsa.

Yayin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, a lokacin ziyarar da ya kai kasar Paraguay a jiya Asabar, babban jami’in diplomasiyyan na Amurka, ya ce, zaben da shugaba Maduro ya ce lashe, zabe ne da aka tafka magudi.

Pompeo ya kara da cewa, kasashen duniya 54, sun amince da jagoran ‘yan adawa Juan Guido, a matsayin shugaban wucin gadi na kasar ta Venezuela.

Ya kuma zargi Maduro da yin amfani da Rasha da Cuba da kuma China, wacce ya ce tana bai wa jami’an kasashen yankin kudancin Amurka cin hanci domin samun biyan bukatun kanta.

Ya ce “Irin harkokin kasuwancin da China ke yi a yankin Kudancin Amurka, na da babbar alaka da manufofin tsaron kasarta da burinsu na bunkasa fannin kere-kerensu zamani da kuma satar fasahohi.”

Pompeo ya kara da cewa, Amurka na da burin ta ga China ta ci gaba, amma ba ta bin wannan tafarki ba.