Qatar 2022: Ronaldo Zai Fara Tallata Kansa A Gasar Cin Kofin Duniya

Cristiano Ronaldo

Wannan shi ne karo na biyar da Ronaldo yake zuwa gasar cin kofin duniya, ta kuma yi wu, shi ne karo na karshe.

Ga dukkan alamu, dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, zai yi amfani da gasar cin kofin duniya da ke wakana a Qatar wajen tallata kansa ga kungiyoyin da ke sha’awar sayensa.

A ranar Talata Manchester United ta raba gari da Ronaldo, bayan wata zazzafar hira da ya yi, inda ya caccaki kocin kungiyar ta United da shugabanninta.

Dan shekara 37, Ronaldo, wanda yanzu haka ba shi da kungiya, zai jagoranci tawagar Portugal wajen karawa a wasansu na farko da Ghana.

Wannan shi ne karo na biyar da Ronaldo yake zuwa gasar cin kofin duniya, ta kuma yi wu, shi ne karo na karshe.

Wasan na Portugal da Ghana zai wakana ne a filin wasa na Stadium 974 a Doha, babban birnin Qatar a ranar Alhamis.