Ra’ayin ‘Yan Najeriya Kan Shirin “Gyara Halinka” Na Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya

A wannan makon ne, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya, ta kaddamar da wani shirin sauya akalar tunanin jama’ar kasar domin samun ci gaba.

Shirin dai ya ta’allaka ne akan gyara hali daga kan kowane dan kasar ta Najeriya da zimmar ganin kowa ya ba da tasa gudunmuwar wajen gina kasa.

Masu lura da al’amura sun ce, shirin ya yi kama da wanda gwamnatin Buharin ta fitar a lokacin ana mulkin soji, wanda aka yi mai lakabi da War Against Indiscipline (WAI), wato yaki da rashin da’a.

Wasu kuma na ganin shirin bai zo a lokacin da ya dace ba, lura da cewa ‘yan kasar na cikin mawuyacin hali.

Dangane da haka wakilin Muryar Amurka, Hassan Umaru Tambuwal da ke Ibadan ya ji ta bakin wasu ‘yan Najeriya:

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’ayin ‘Yan Najeriya Kan Shirin “Gyara Halinka" Na Buhari” –‘2”35