Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Najeriya Kan Shugabancin Buhari

Yayin da gwamnatin Mohammadu Buhari ta jam’iyyar APC ke cika shekaru biyu kan mulki, ‘yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkancin bakinsu game da rawar da gwamnatin ta taka a shekaru biyu da suka gabata.

A lokacin da wasu ‘yan Najeriyar ke ganin an sami ci gaba a wasu bangaren, ta wasu bangaren kuma abin ba haka yake ba. musamman idan aka duba harkar tsaro a kwai ci gaba sosai.

Sai dai kuma a yayin da wasu ke ganin an ci gaba, wasu kuma na kushewa tare da bayar da shawarwarin ta yarda za a kawo karshen matsalolin da gwamnatin ta gada daga gwamnatin da ta shude.

Alhaji Sa’idu Baba Gombe, na ganin cewa a halin da ake ciki yanzu zai yi wahala a samu mutumin da zai iya fadawa shugaba Buhari gaskiyar halin da ake ciki a Najeriya.

Fatan ‘yan Najeriya dai shine ganin gwamnati ta karbi shawarwarin da ake gabatar ma ta, na jan ‘damara domin tunkarar matsalolin da keg aba kafin zaben shekara 2019.

Saurari rahotan Babangida Jibrin domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Najeriya Kan Shugabancin Buhari - 2'45"