Ra'ayoyin 'Yan Najeriya Kan Kasafin Kudin Bana

Mukaddashin shugaban Najeriya, Prof. Yemi Osinbajo

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu dangane da kasafin kudin bana da mukaddashin shugaban kasa Prof. Yemi Osinbajo ya rattabawa hanu bayan da shugaba Muhammadu Buari ya amince da kasafin kudin.

Da yawa daga cikin ‘yan Najeriya sun jima suna dakon wannan kasafin kudi domin ganin yadda zai shafi rayuwarsu ta yau da kullum.

A jiya Litinin Osinbajo ya saka hanu a kasafin kudin a gaban wasu mukarraban gwamnati da suka hada har da shugaban ma’aikatan Fadar shugaban kasa, Abba Kyari da shugaban Majalisar dattawa Dr. Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara.

Jumullar kudin da za a kashe a wannan shekara ya kama naira triliyan 7.44.

A ranar 19 ga watan Mayu Osinbajo ya karbi kasafin kudin daga majalisar tarrayar kasar.

An kuma ta sa ido a ga wanda zai sa hanu a kasafin kudin lura da cewa shugaba Buhari na London ya na jinya.

Wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal dake Ibadan ya jiyo mana ra’ayoyin wasu daga cikin ‘yan Najeriya dangane da wannan kasafin kudi.

Saurari rahotonsa domin jin cikakken bayani kan lamarin:

Your browser doesn’t support HTML5

Ra'ayoyin 'Yan Najeriya Kan Kasafin Kudin Bana - 2'47"