Ranar Tunawa da Masu Dauke da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki.

A yau ne ranar da hukumar kiwon lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da mutanen dake dauke da cuta mai karya garkuwar jiki a duk fadin duniya.

Dandalin VOA ya zanta da Komarad Nuhu Sulaiman Gaya shugaban kungiyar masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki ta jihar kano, ya kuma bayyana mana matsalolin da suke fuskanta a kungiyance.

Nuhu Sulaiman Gaya dai ya bayyana wannan rana a matsayin ranace da aka ware domin tsayadda tsangwama da tsana wato yadawo an dainayi baki daya, yakuma bayyana cewa kungiyar na cigaba da aiki wajen ilmintar da kuma wayar da kan al’umma kan dakatar da tsangwamar ga masu dauke da wannan larurar, domin tsangwama na daya daga cikin abin da yake kawowa wannan larurar take karuwa, rashin tsangwamar kuma na iya jawowa yaduwar cutar ta ragu.

Matsalolin da kungiyar ke fuskanta shine rashin kayan gwaje gwaje, da taimako daga kananan hukumomi ga irin wadannan kunguyoyi. Shugaban kungiyar dai ya bukaci gwamnati da masu ruwa da tsaki da su taimaka musu domin kawo karshen wannan cuta a jihar Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Ranar Tunawa Da Masu Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki - 2'59"